7 February 2016

[Kannywood] An Fitarda Jarumai Uku Daga Cikin Maza Da Mata Wadanda Zasu Iya Zamowa na daya a Wannan Shekara


An fitar da jerin sunayen 'yan wasa da fina-finan da za su iya samun lambar yabo ta Kannywood.

'Yan wasa ukun da aka ware don bai wa daya daga cikinsu Gwarzon Dan Wasa a bana su ne Sadiq Sani Sadiq saboda hazakar da ya nuna a fim din "Bayan Duhu" da Adam A. Zango saboda rawar da ya taka a "Gwaska" da kuma Ali Nuhu saboda basirar da ya nuna a "Nasibi".

A bangaren kyautar Fitacciyar 'Yar Wasa kuma, wadanda aka zabo su ne Jamila Umar, wacce aka fi sani da Jamila Nagudu saboda ficen da ta yi a "Na Hauwa" da Rahama Sadau "Halalci" da kuma Nafisa Abdullahi "Baiwar Allah".

Sauran wadanda aka bayar da sunayensu da suka cancanci samun kyauta su ne:

Dan Wasa Mai Rufa Baya: Lawan Ahmad "Da'iman", Sadik Ahmad "Nasibi", Ali Nuhu "Rumfar Shehu".

'Yar Wasa Mai Rufa Baya: Ladidi Fagge "Da'iman", Fati Shu'uma "Basma", Fati Washa "Hindu".

Sourced By BBC Hausa



0 comments

Post a Comment