13 March 2016

[Kannywood] Jarumi Sadik Sani Sadik Da Nafisa Abdullahi Tareda Umar M SharifSun Samu Nasarar Gwarzon Wannan Shekarar


Jarumi Sadik Sani Sadik Da Nafisa Abdullahi Tareda Umar M SharifSun Samu Nasarar Gwarzon Wannan Shekarar

Fitaccen dan wasan Fina-finan Hausa, wato Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya lashe kyautar jarumin jarumai a karo na biyu a jere.

An sanar da hakan ne a wajen taron karrama 'yan Fim da aka yi ranar Asabar da daddare a Abuja, babban birnin Najeriya.
Dan wasan Fim din ya lashe kyautar ne saboda rawar da ya taka a Fim din "Bayan Duhu".

Kazalika Nafisa Abdullahi ce ta yi nasarar zama jarumar jarumai a bangaren mata sakamakon
rawar da ta taka a Fim din "Baiwar Allah".

Sauran wadanda suka yi nasara su ne Sulaiman Yahaya Bosho, wanda ya lashe kyautar "Dan wasan Barkwanci", yayin da Maryam Baba Asin ta yi nasara a matsayin "jarumar jarumai a rukunin kananan yara" sakamakon ficen da ta yi
a Fim din "Basma".

Ali Gumzak ne ya lashe kyautar "Gwarzon Darakta ", yayin da Haruna Talle Maifata ya lashe
kyautar "Dan wasan da ya fi mugunta".

Lawan Ahmed ne ya yi nasara a fannin "Dan wasan da ya taimakawa babban jarumi" a Fim din "Da'iman", yayin da Fati Shu'uma ta yi
nasara a matsayin " 'yar wasan da ta taimakawa babban jarumi" a Fim din "Basma".

Umar M. Sheriff ne ya zama "Gwarzon mawaki". Fitattun jarumai da ministoci da kuma masana na
cikin wadanda suka halarci bikin.

Ga dai abin da wasunsu ke cewa bayan da aka basu wannan lambar yabo.



0 comments

Post a Comment