30 December 2016

Jarumi Adam A Zango Ya Bayyana Cewa Fina Finai 20 Kacal Zaiyi A Wannan Shekarar 2017


Fitaccen Mawaki kuma shahararren Jarumi Adam A. Zango ya baiya cewa a shekara ta 2017 fim 20 zai yi kawai, Fim 20 din sun hada dana wasu furudusas, yace guda 8 na kamfaninsa sannan 12 daga wasu furudusas din, yace yin hakan ne zai bashi daman kara kula da wasu bangarorin da yasa gaba na harkokinsa na yau da kullum harda wakoki da yakeyi. Babban fim din da Jarumin zai yi wanda ba'a taba kamansa ba shin MADUGU a wannan shekara wanda zai kashe sama da miliyan 10.

A farkon shekara ta 2017 ne zai kaddamar da kungiyarsa wanda zai dunga taimakawa al'umma marasa karfi, yace yin wannan kungiya yana son ya mai dawa al'umma taimakon da suke ma masana'antar domin yin hakan ne shima zai bada tashi gudumar ga al'umma. Kungiyar tashi mai suna ZANGO INTERVENTION INITIATIVE FOUNDATION wanda tuni an mata rijista kuma ya fara tallata manufofinsa na wannan kungiya a shafinsa na Instagram da sauran shafukansa na sada zumunta a yanar gizo.

DAGA SHAFIN :Kannywood Today



0 comments

Post a Comment