14 December 2016

Jaruma Hafsat Idris Wacce Akafi Sani Da Barauniya Tace Bazata Iya Fitowa A Matsayin Karuwa Ba A Fim


Ta fito barauniya a film, amma tace baza ta iya fitowa a karuwa ba!

Hafsat Idris, wadda a industiri akafi sani da Barauniya, jaruma ce data shigo industiri da kafar dama. Ana iya cewa ta taka sahun Rahama Sadau. To amma fa nata takun ba irin na Rahama bane. Domin kuwa ita Hafsat ta amsa lakabin ta na Barauniya, tun bayan bayyanar ta acikin fim din Barauniya, kyakkyawar jarumar ta sace zuciyar furodusoshi, daraktoci,’yan kasuwa da ‘yan kallo. Yanxu haka babu wata jaruma da ta kai ta yawan aiki film a gabanta. Kowa na rububin saka ta a fim saboda yadda ta taka rawar gani a cikin fim din Barauniya ta yadda da alamu nan gaba kadan zata doke duk wata jaruma da keji da kanta a yau.

Wakilin mu ya tattauna da Hafsat Idris game da yadda akayi ta shigo harkar fim da kuma inda tasa gaba, da sauran wasu bayanai.

TAMBAYA: HATSAT KI FADAWA MASU KARATU TARIHIN RAYUWARKI A TAKAICE? 

AMSA: Suna na Hafsat Idris. Takaitaccen tarihi na shine an haife ni a garin shagamu a shekarar 1982. Nayi makaranta firamare da sakandare na duk a shagamu.

TAMBAYA: ME YA BAKI SHA’AWAR SHIGA HARKAR FIM?.

AMSA: Abin ya kan banj sha’awa kuma harkar fim na burgeni. Sannan naga da zaman dana keyi, ya kamata na fara harkar, saboda sana’ace, in dai har zasu iya dauka na. Kuma cikin ikon Allah gani na fara harkar.

TAMBAYA:YAUSHE KIKA SHIGO INDUSTIRI?

AMSA: Na shigo masa’antar fim a watan augusta na shekarar 2015.

TAMBAYA:KASANCEWAR KI SABUWAR 
JARUMA, YA KARBUWAR KI TA KASANCE?

AMSA: To gaskiya Alhamdulillahi! Babu abinda zance sai godiya ga Allah saboda bani nake fadi ba, su suke fadi. Gaskiya nima nasan na samu karbuwa. Amma daga Allah ne. Domin da shigowa ta industiri wata na bakwai kenan,nayi fim sunfi guda ashirin, kuma dukkan su babu fim din banza.

TAMBAYA:KO ZA IYA LISSAFA MANA KADAN DAGA CIKIN FINA FINAN DA KIKA YI?

AMSA:To, a cikin fina finan da nayi akwai,
1-Barauniya, 2-Dan kurma, 3-Alkibla, 4-Furuci
5-Haske Biyu, 6- Ankon Biki, 7- biki Buduri, 8- Ta Faru Ta Kare, 9- Mu Zuba Mu Gani, 10- ‘Yar Fim, 11-Labari Na, 12-Iftala’i da dai sauransu.

TAMBAYA:ANCE KIN TABA YIN AURE,SHIN GASKIYA NE?.

AMSA: Eh,hakane, na taba aure.

TAMBAYA: KIN TABA HAIHUWA?.

AMSA: Eh na haihu, ina da yara.

TAMBAYA:YARAN KI NAWA?

AMSA: Wannan sirri na ne, ba sai kaji ba.

TAMBAYA:KO KINA DA NIYYAR SAKE WANI AURE YANXU?

AMSA:Kasan Allah shi ke tsarawa mutum rayuwar sa. Saboda tun farko bansan cewa zanyi fim ba. Allah ne ya kaddara min cewa sai na taka wannan rawa. To kuma ni ‘Yar musulmi ce. Kuma aure ne ya haife ni, ko nayi suna a fim ko banyi ba, ina fatan Allah ya bani miji nagari nayi aure.

TAMBAYA: YA KIKE KALLON RAYUWAR KI A MATSAYINKI NA JARUMAR FIM?

AMSA:Gaskiya ina jin dadi irin yadda aka dauke ni. Ni dai babu abinda zance sai godiya ga Allah.

TAMBAYA: YAYA KIKE KALLON RAYUWAR ‘YAN FIM DIN HAUSA?

AMSA:Gaskiya ni ban same su da wata matsala ba. Saboda duk yadda ka dauki rayuwarka, haka zaka tafi da ita. Ni dai zan mutunta duk wanda na tadda a harkar na sama na da kuma na kasa dani.

TAMBAYA:WANE MATSAYI KIKE SO KI KAI A WANNAN HARKA?

AMSA:Kasan ni ba zan iya cewa ga matsayin da nake so na kai ba. Saboda Allah shike tsarawa, duk abinda ya tsarawa rayuwa ta ya riga ya gama. Saboda haka duk abinda Allah Ya tsarawa rayuwata dai dai ne, dama haka yaso ya ganni.

TAMBAYA:WANE JARUMI KO JARUMA KIKA FI SON A HADA KI DASU A FIM?

AMSA:To,ni gaskiya duk wanda aka hada ni aiki dashi ina jin dadin aiki dashi.

TAMBAYA:WADANNE NASARORI KIKA SAMU DAGA FARKON SHIGOWAR KI HARKAR FIM ZUWA YANXU?

AMSA:Na Samu nasarori bila adadin, sai dai inyi godiya ga Allah.

TAMBAYA:WANE KALUBALE KUMA KIKA FUSKANTA?

AMSA:Gaskiya na dan samu matsala, kasan ba yadda za’ace mutum ya shigo masana’anta bai samu matsala ba. Amma ni irin ace wai na shigo na wahala, ina bin mutane da dama neman aiki,gaskiya ni banyi irin haka ba.

TAMBAYA:KO KIN SAMU MATSALA A GIDAN KU LOKACIN DA KIKA SHIGO HARKAR FIM?

AMSA:Dole ne duk wanda ya samu kansa a wannan hali zai iya samun matsala ko a gidan su a ji irin ba dadi. Amma daga karshe ina nuna masu wannan fim din fa sana’ace sannan idan ka tafi yin shi waya ma baka iya dauka balle ka samu damar zuwa yawo. Kuma ina son mutane su sani, fim sana’ace kuma ko wace masana’anta akwai nagari akwai kuma na banza. Idan ka tsare kanka Allah zai taimake ka, saboda kai dai kasan me kaje yi, idan kaje iskanci ne kai kasani, idan ma kaje a wulakance ne kai kasani idan kuma kaje da mutuncinka Allah zai kare maka mutuncinka.

TAMBAYA:KINA GANIN AKWAI MATAKIN DA BAZA KI IYA TAKAWA BA IDAN AKA BAKI A Fim? 

AMSA:Gaskiya so tarj da yawa ina yawan fadin cewa bana bad role. Amma ba yadda zaka iya idan kana so ka zama jarumi duk abin da aka zo maka dashi dole ka hau shi, tunda kowa yasan wasa ne. Amma ni dai ra’ayina bana son bad role gaskiya.

TAMBAYA:KINA NUFIN AKWAI BAD ROLE DIN DA IDAN AKA BAKI SHI BAZA KI IYA HAWA BA?

AMSA:E, gaskiya, yanzu misali irin ace na fito a karuwa, gaskiya bazan iya ba. Saboda ina son na tsira da mutunci na.

TAMBAYA:SHIN ANA BIYAN KI YADDA YA KAMATA KO KUMA SAI A HANKALI?
AMSA:E,Alhamdulillahi,ana biya na. Idan nayi aiki, ina gamawa ake bani abinda Allah ya sauwake. Kuma na karba nace Allah ya sanya masu albarka saboda nasan hakki na ne.

TAMBAYA:ANA CEWA IDAN ‘YAN FIM SU KAYI SUNA SAI SU FARA JI-JI DA KAI DA GIRMAN KAI,SU RIKA WULAKANTA MASOYAN SU.KE KUMA NAN GABA YA RAYUWAR KI ZATA KASANCE?.

AMSA:Gaskiya ni bana fatan nayi haka. Saboda shi dan’adam daraja gare shi. Kuma duk yadda kazama a rayuwa nan baka taba tunanin zaka kai ba. Gaskiya ni bana burin na wulakanta wadanda suka taimaki rayuwa ta,da ma wadanda basu taimake ni ba.

TAMBAYA: KO KINA DA SAKO GA MASOYAN KI?.

AMSA:To, Alhamdulillahi, yanxu dai tun ban je ko’ina ba ina samun masoya ta ko’ina ana kira na a gaisa dani. To masoya na maza da mata ina masu fatan alheri.
Labari daga mujallar hausa fim.



0 comments

Post a Comment