6 February 2016

[Littafi] Halaccin Sarauta Kashi Na Daya


==>Aliya yar kimanin shekara ashirin da daya zaune adakinta wanda yasha kaya,duk abinda ya'mace budurwa zata bukata toh akwai shi acikin dakin aliya takardune agabanta dakuma hotunan mutane wanda take bi daya bayan daya daga dan zaman da ni benaxir nayi ina lekenta nasamu
labarin cewa Aliya yar asalin garin yombi ne wata babbar masarauta da ake darajar mulkin
sarauta,tanada shekara sha biyar sarkin yombi ya bukaci akashe duk masu hannu da reshawa wanda acewarta sarkin yabada sakon akashe mahaifinta mussaman acikin wannan hargowan don mahaifinta yakasance shine galadima kuma yana kawo musu matsala a fadan garin, duk wani
abu marar kyau mahaifin aliya hassan adamu yana kokarin yafidda hakkin musulunci dakuma hakkin mutane.

Hakan yasa sarkin garin yabukaci da akasheshi cikin saa aka kashe
hassan adamu da matarsa alokacin aliya tana makarantan kwana na yan'mata dawowarta ta
tarar da mai aikinsu wanda yabata wani karamin akwati acewarsa ana gobe mahaifin zai rasu yace
abata, tayi kuka sosai harta bude akwatin anan tasamu takaranta tarihin komi mahaifinta dama
yasan zaa kasheshin donhaka yamata bayanin komi,

dawannan aliya tayi alkawarin saita rama wa iyayenta abunda aka musu, barin garin tayi ta tafi abuja gurin yar mamanta inda ta kammala
secondry dinta a shekara sha shida, sannan tasamu admsn a g.s.u ta takaranta sociology na shekara hudu sannan taje tayi service dinta,ta kammala komi tanada shekara ashirin da daya, duk wannan tsawon lokacin aliya bata saurayi
namiji da sunan soyayya ba acewarta zaibata mata duk wani plans din ta, yar mamanta wacce tazauna agunta tasan da maganan ramakon da aliya takesonyi kuma tagoya mata baya duk da
tana tsoro anma taga ita aliyan bata tsoro.

aliya agun bautar kasanta wanda tayi a benue tasamu nasaran samun wani mai suna ikem zama tayi
tayu training agunsa, yakoya mata fada, yakuma koya mata duk dabaru da abubuwan dake faruwa acikin gidan sarauta, ya ilmantar da ita da
basira dakuma dabaru dazata kare kanta takuma yi ramakonta cikin kwanciyan hankali, yabata littafan tarihi dakuma littafan koyan basira da littafan daya shafi sarautan hausawa harna yare aliya takaranta tsaf takoya, saan da aka samu
shine aliya macece mai hazaka da basira, batada mantuwa ko kadan, kallon abu sau daya yakansa ta haddaje abu batare da ta mantaba, sai abun yasamu daidai sanadin karanta sociologyn datayi.

saita zamto mai nutsuwa gurin karanta mai dan adam yake ciki yake kuma sonyi, saidata
kammala komi sannan ta tattara takoma gidan antynta inda tafara shiri antynta tamata waazi
anma aliya tanuna tafiyan shikadai zaisa tamutu lafiya, tabarta aranan aliya ta tattara tatafi yombi
inda tasamu daki tajera kayan alatu dakomi. Dakin yana wani lungu ne wanda bakowa bane
zaikawo akwai abun duniya aciki, aciki tazauna tagama hargowanta agarin yombi tana tara labarai gameda fadan sarki.

Tahado kan matarsa,da yaransa daduk wani abu daya shafi
sarkin, sannan tadau niiyan shiga fada, Dafarko taje tasamu matar dake kwasan bayi takai fada,taroketa datanason zama afada akan acewa ita yar kwarkwara ce anma batasan wacece
ba,tanason tazauna as baiwa don tagane ahankali dafarko taki yarda anma da aliya tacire dubu goma tabata bashiri tace "kije kisaka kaya irin nasu na bayi mushiga" aliya ta amince da hakan takoma gyda tashirya tsaf tanemo wasu
tsoffin kaya tasaka, sannan tanufota, matar tace "muje kishiga cikinsu karki fadawa kowa komi,
kina gama nemo mahaifiyarki karki manta dani" aliya ta amince dahakan ita burinta tashiga fadan sarki takashe sarki.

Dahaka suka shige kafanta na dama tafara shiga fadan tare da adduan Allah yabata saa, gefen fannin bayi aka kaisu anan aka bukaci da su zazzauna, akasa suka zauna aliya
tajuya tana kallon wurin dakyau takuma kalli bayin dake gefenta kowannensu kuka yake don basuda niyyan zuwa ita kuwa ko ajikinta, acan saiga matar tashigo tareda wata wacce taji tana kira da "umma uwar soro" umma uwar soro tace
duk sumike acewarta zata rabasu ne zata zabi masu aiki a fada, da masuyi a kicin, da na bandaki, dakuma sauran kwarkwaraye dafarko ta umurci kowacce taje tayi wanka aka basu wani farin riga susaka, aliya tayi wankan tsaf sannan tafito tajera layin ana dubiya ne daga fatan jikinsu, sai kuma kyansu, da yanayin tsayinsu, tafara bi daya bayan daya inta yanke awani gu zakiyi aiki zaabaki uniform din aikin gurin kodata iso kan aliya takare mata kallo , aliya doguwa ce
bawanda zaice guntuwa ce, saidai bakace ,bakinta mai kyau, tanada hanci dan daidai da
karamin bakinta sai manyan ido, hakika black beauty ce don yanayin fatarta baacika samun irin
shiba, hannun hajjo tarike dasauri takalleta tareda cewa "anya ke baiwa ce?"

Aliya tayi murmushi don dama tashirya wa tambayan tace
"fatana na gado ne" umma uwar soro tacigaba da dubata gashin hajjo acunkushe cikin ribbon ta
cire ribbon dim saiga gashi yazubo har gadon baya, ta girgixa kai sannan tace kumika mata uniform din fada, anan aka bata blue yard ne anyi dogon riga fittet, sai dankwalin dan karami hajjo
daure kanta tayi duk kokarim ta cunkushe gashin abun ya gagara. Aka kaita masaukin bayi
aka nuna mata katifanta, dakin ko na karnuka albarka don baida fasali ko kadan anma yata iya? Tadau niyya, tana zaune ta gefenta tafara
hararanta aliya bata kulata ba can dai tamiko tareda cewa "keeh zoki wankemim kafa ga dutsen ce" aliya takalleta sannan tajuya tacigaba
da abunda take yarinyan ta tashi kamo gashin aliya tayi tasake mata mari wanda ya nutsar da sauran bayin yakuma janyo hankalinsu tace
"nace ki gogemin kafa" wata dake gefe tacewa aliya kiyi fa.

Itace shugabanmu anan aliya bata
musa ba ta tsugunna ta goge sannan tamike.
Azuciyanta tace duk zansami lokacinku bata kanku nake ba yanzu,ananne umma uwar soro tashigo dakin sannan tace tunda munsamu sabbin bayi aikin naku zai canju,keh meye sunanki? Aliya tace "aliya" tohm dake aliya dake
bilki zakuna isa gun yarima yusuf, sauran kuma duk kunsan wurin zuwa" ficewa tayi alokacin ita
bilkin taja aliya tareda cewa "baki taki saa ba daga zuwa sai gun yarima yusuf? Bama yarima
abdullahi ba.

Tafdi zakisha wulakanci dan
wulakancine anma yaka iya kana talaka dakai," aliya bata furta komiba don ko bilki bata fada
mataba tasan waye yarima yusuf bashi kadai ba kowa afadan saidatasani takumasam mezasu iya aikatawa donhaka tashirya wa yusuf, bilki ce tace tashi muje sunmike tsum suka nufi kicin kowacce tadauki tray sannan suka nufi fannin yariman aliya tana hankalce dakomi duk tafiyan
dasukeyi,sun nufi kofan inda dogarai biyu suke tsaye akofan bilki kai akasa tace "mun isowa da yarima abinci" daga ciki yace " kushigo" dogaran ne suka basu wuri suka shiga falone babba yasha duk wani kayan alatu dayakamata ace
saurayi dan sarki yasamu. Yana kwance akan kujera, suka sunkuyar dakai suka mika abincin
kan dinning sannan sukaja gefe suka tsaya, wannan ma aladace bazasu bar falon ba harsai yarima yagama cinye abincin, mikewa yayi yanufivkan dinning din yana kallon abincin daya bayan daya,bilki tana rike da serving spoon tazuba
mishi friedrice din sai yamballs da ferfesun kayan ciki, zobo ma tazuba mar akofin yana danne wayarsa wacce aliya takare masa kallo, dogo ne wankan tarwada yanada faffadan kirji,manyan idanuwa wanda taga alamun kaman shine gadon
gydansu dogaye ne masu manyan idanu,yanada dan dimple saidai baya murmushi wannan dama
tasani tundaga farko, ayadda ta karanceshi akwai alamun damuwa atattare dashi wanda yaboye babu wanda yasani, wannan damuwan
itace ke hanashi sakewa har yake matsifa da fadace fadace don baida abunyine ,loneliness yamar yawa, harya gama ci baiyi magana ba
yamike yakoma kan kujera dama tashan bbc yake kalla, har alokacin yana danna waya sun tattara abincin sannan suka fito dakinsu suka nufa.

Aliya tadanci abincin kadan wanda su bayi suke samu dama asalinta bamai ci bane hakan
yasa tazama siririya sai uban kiran jiki.

Zamu Cigaba Insha Allah

Source by NovelTime.Tk



0 comments

Post a Comment