20 March 2017

An Konewa Fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Gida


Fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu wanda akafi sani da Rarara Jami’ar waka yace shi ba wanda yake zargin da sun kone mashi gida. Amma abinda yasani shine, koma su waye to tabbas makiyansane kuma makiyan jahar kano. Domin duk mai kishin kano ba zaiyi ta addanci ajahar kano ba. Kuma ni nasan rubutaccen abu fararren abu, duk abinda Allah ya rubutu zai faru tole sai ya faru.
.
Kuma dama rayuwar mawakin siyasa kullum acikin nemanta makiyya suke yi. Koda nayiwa Gwabna Ganduje Khadimul Islam waka, ko banyi masa waka ba to makiyya ba zasu kyale ni ba. Dan haka wannan ba bakon abubane. Kuma wannan zan iya lissafa shi yana da nasaba da nasarar dana samu aduniya.
.
Ni nasan da arzuki da karatu da basira duk na Allahne to tunda Allah ya bani basira dole na fito na nunawa duniya irin baiwata. Kuma abinda nakeso mutane su gane acikin sirrin zuciyata bana gaba da kowanne dan siyasa. Aikina nake nunawa duniya ba tozarta wani mutum ba.
.
Nasan wadanda suka kone min gida ni suka so su kone amma Allah bai yarda ba. Kuma nasan tabbas, ba zasu daina farautar rayuwata ba. To, inayi masu albishir da cewa idan lokacina yayi zan mutu ba sai sun wahalar da kansu ba, idan kuma lokacina bayyi ba to koda zasu saka ni cikin turmi su daka, to saina rayu. Inji Dauda Kahutu Rarara (Jami’ar Waka).0 comments

Post a Comment