6 April 2017

Jaruma Rahama Sadau Ta Karo Wulakanci Ku Kalli Wasu Sabbin Hotuna Masu Zafi Da Tayi


Fitacciyar jarumar Kannywood da aka fi sani da suna Fina finan Hausa, Rahama Sadau ta sake sakin wasu zafafan hotunan ta sanye da wasu kayatattun kayan ado da kwalliya.

      
Kalli wasu kyawawan Hotunan ta Rahama Sadau Kamar yadda Hausatop.com ta ruwaito, Rahama mai shekaru 23 ta dauki hoton ne sanye da wasu irin kayan turawa tare da bakin damara data daure kwankwasonta da shi.

Kalli wasu kyawawan Hotunan ta Rahama Sadau Idan za’a iya tunawa a shekarar data gabata ne dai hukumar yan wasan Hausa ta dakatar da Rahama Sadau daga shirya fina finai sakamakon wani bidiyon waka data fito a ciki na wani mawaki Classiq, inda hukumar tayi zargin anyi rungume rungume a cikin bidiyon.

Sai dai duk da wannan dakatarwa da aka yi ma Rahama, bata yi kasa a gwiwa ba, ta yadda hukuncin ya zame mata tamkar gobarar titi a Jos, sakamakon gayyata data samu zuwa kasar Amurka daga fitaccen mawakin nan Akon. Amma zuwa yanzu ba’a tabbatar da ko hukumar shirya fina finan zasu dawo da Rahama ba ko a’a. lokaci ne kadai zai iya tabbatar da hakan.

Daga hausa naij.com
0 comments

Post a Comment