16 April 2017

Jaruma Rahama Sadau Tace Tun Tana Yarinya Karama Batada Burin Daya Wuce Tazama Yar Rawa (Dancer)


Tsohuwar Jarumar kamfanin shirya fina-finan Hausa wato (Kannywood) Rahma Sadau tace tun tana Yarinya yar Karama bata da wani Burin daya wuce ta zama me yin Rawa.

Jaruma Rahma Sadau ta bayyana haka a wata hira da tayi da daya daga cikin Gidajen Talabijin na Arewacin kasar nan.

Tace tana kasancewa cikin nishadi duk lokacin data samu kanta tana yin Rawa, gashi kuma yanzu ta wuce matsayin Rawa ma.

Idan baku manta ba yanzu haka hukumar ladabtarwa na kamfanin shirya Fina-finan Hausa wato Moppan ta dakatar da Jarumar daga fitowa cikin shirye-shirye fina-finan Hausa tun bayan wani faifaiyin bidiyo daya fito wanda Jarumar tayi waka da wani mawaki me suna Classic.
0 comments

Post a Comment