3 April 2017

Kannywood: Jaruma Maryam Booth Ta Bayyana Dalilin Dayasa Ta Rage Fitowa A Fina Finai


Shahararriyra ‘yar wasan Kannywood, Maryam Booth ta bayyana cewa ba a ganin ta a fina finai a kwanakin nan saboda komawa karo karatu da ta yi.

A wata hira da jaridar Premium Times ta yi da ita, jarumar ta bayyana cewa ta kammala karatunta na Difloma a jami’ar Bayero ta Kano, da digirin farko a kasar Malaysia a fannin kasuwanci, kuma yanzu haka ta na yin digirin ta na biyu wato Masters.

Jarumar mai shekaru 23 a duniya ta bayyana cewa da zaran ta kammala karatun nata za ta dawo harkar fim gadan gadan, domin kuwa babu wani abu da take sha’awar yi da ya fi shi.

Haka kuma ta yi tsokaci akan irin ‘yan sana’o’i da ta ke yi a gefe, inda ta ce yanzu haka ta na da shagon kwalliya mai suna MBooth beauty Parlour, ta ce ta na kuma da kudirin bude makarantar koyan shirya fina finai a jahar Kano.
0 comments

Post a Comment