12 April 2017

Kannywood: Magulmata Sun Fusata Jaruma Hadiza Gabon


Hadiza Gabon ta aike sakon ne ta shafinta na Instagram

Fitacciyar 'yar wasar Hausan nan Hadiza Gabon, ta yi gargadi ga magulmata masu yawan magana a kan 'yan wasan Hausa a shafukan sada zumunta.I'll

Hadiza ta aike da sakon ne ta shafinta na instagram inda ta ce, "Ina mamakin yadda mutane suke shiga abin da babu ruwansu."

Ta kara da cewa, "Masoyinka ba zai zage ka ba, sai dai ya baka shawara, kuma mu 'yan wasan Hausa muna maraba da shawarwari daga wajen masoya amma bai kamata mutane su dinga gulmace-gulmace da fadin abubuwan da bai shafe su ba.

Gabon ta ce ya kamata mutane su bi koyarwar addinin Musulunci su daina gulma da bin diddigin da ba huruminsu ba da kuma shiga sharo ba shanu.

Ta dai yi wannan magana ne sakamakon yadda wasu mutane ke aikewa da sakon zagi da cin zarafi a duk lokacin da 'yan wasan suka sanya wani abu da ya shafe su a shafukan sada zumunta.

Hadiza ta ce, idan ma gyara ake so a yi musu to ya kamata a yi cikin girmama juna da fahimta.
0 comments

Post a Comment