9 April 2017

Jaruma Rahama Sadau Tace Tanason Yan Wasan Kwallon kafar Barcelona Messi da Neymar


Jarumar Fina-finan Hausa Rahama Sadau na son yan wasan kwallon kafar Barcelona, Messi da Neymar, ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram bayan da ta saka hoton yan wasan su biyu dauke da alamar da take nuna soyayya ga yan kwallon kafan.

A ranar larabar data gabata ne dai kulob din na Barcelona ya doke abokin karawarsa na PSG daci 6-1 a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, wasan da ya kayatar da yan kallo matuka.
0 comments

Post a Comment