11 April 2017

Kannywood: Tattaunawa Ta Musamman Tareda Jaruma Hadiza Gabon Kai Tsaye


Jaruma Hadiza Gabon tace tanason tayi Aure amma lokacine kawai bai yiba.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da sukayi da Shafin BBC HAUSA, Inda jarumar ta bayyana aure da cewa lokacine tamkar na mutuwa, Idan Allah ya kawoshi babu yadda Mutum zai guje mata.

Inda jarumar ta kara da cewa, wallahi babu macen da zata so lokacin Aurenta yayi amma taki yi.

Ita dai jaruma Hadiza Aliyu Gabon itace jarumar data lashe babban kyautar jarumar da tafi tallafawa babban jarumi a film wato Best Actor na African Films Award na bana, Kuma jarumar ta kara jadda da aniyarta kamar kullum na mika sakon godiya ga duk daukakin Masoyanta.

A nashi bangaren jarumin jarumai Wato Ali Nuhu Wanda Ake Yiwa Lakabi Da Sarki A Masana'an tar shirya fina-finai na Kannywood ya yaba da yadda jaruma Hadiza Gabon ta koyi harshen Hausa da turanci da kuma irin rawar da Jarumar ke takawa a fagen shirya fina-finai.
0 comments

Post a Comment