15 April 2017

NEWS: Anyiwa Wani Sanata Dukan Tsiya


*Masari Ya Sha Ruwan Duwatsu.

Sanata ABU IBRAHIM mai wakiltar yankin FUNTUWA ya sha mugun duka a garin Funtuwa  tare da yayyaga masa kaya. Majiyar Sarauniya ta jiyo cewa, sakamakon neman ceton kai Sanatan ya afka motar Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, wanda hakan ya sa hasalallun matasan suka rika yi wa motar ruwan duwatsu har ta kai sun fasawa Sanatan kai. Zuwa yanzu tawagar Masari tare da Sanatan sun garzaya Kaduna domin taron gaggawa akan batun.
0 comments

Post a Comment